Menene bambanci tsakanin Someday da kuma Some day?
Difference between Some day and Someday in hausa
sau da dama mutane sukan shiga rudani a duk lokacin da sukaga wadannan kalmomin guda biyu duba da zamu ga iri daya ne, bambancin kawai shine kalmar farko akwai tazara na biyun kuma babu tazara, saboda haka a cikin wannan shafin zamuyi bayani akan su
SOMEDAY AND SOME DAY
MA ANAR “someday” dakuma “some day”
Someday; na nufin awani lokaci wanda yake ba tabbatacce (ƙayyadajje) ba a gaba (future)
Some day; tana nufin wata rana wadda ba tabbatacaciya ba kokuma (wadda ba a santabaa ) agaba.
Kalmomin sunada ruɗani, dan kuwa bambancin su ƙwalli ɗayane tak wajan rubutu, bambancin kuwa shine tazarar dake tsakanin “some” dakuma “day” (space) kenan.
MENENE MA’A NAR SOMEDAY?
Someday :
Adunƙule “Someday” kalmar adverb ce.
sa annan kuma tana nuni ne ga wani abu dazai faru a wani lokaci wanda yake ba tabbatacce ba agaba .
Misali(i) :
she told me that I would be an adult someday.
(Ta faɗa mun zan zama babba /zan girma wata rana).
Duba ga wannan misalin, zakuga
Maganar da aka faɗi za ta farun, amma ba a ƙayyade(tantance yaushe za a girman ba) .
Misali(ii) :
Someday, I will be an educated person but untill then I will be studying.
(Wata rana zan zama mutum me ilimi amma har izuwa lokacin zan cigaba da karatu)
Toh kunga awannan misalin ma dai lokacin da zai zama mai ilimin, bawai ƙayyadajjen lokacibane.
MENENE MA ANAR SOME DAY?
Some day:
In aka lura da kyau za aga wannan akwai tazara a tsakanin “Some” dakuma “Day” wannan shine ban ban cinta da “Someday” arubuce.
Idan muka ɗauki kalmomin “Some Day” ɗaya bayan ɗaya za muga.
Kalmar “Some” kalmar (adjective) ce, Kumaa tana nufin abu wanda ba ƙayyadajje ba (yawan abu).
Misali ;
I need some water.
(Ina ɓuƙatar ruwa)
To kunga ai ba a ƙayyade yawan (adadin) ruwan ba. Amma idan akace
I need a cup of water.
(Ina buƙatar kofi guda na ruwa)
Kunga ai anan an ƙayyade adadin ruwan (wato kofi guda) kenan.
Sai kuma ma’anar kalmar dai, ita kalmar “Day” kuma noun ce.
To kunga (Adjective) dama tana nuna ya (Noun) take ne
Shiyasa idan akace “Some Day”
Yana nufin wata rana ce, amma wadda ba tabbataciya ba (ƙayyadajjiya) komaa ince ba asantaba.
Misali (i) ;
I am pretty sure he will come some day next month.
(Ina da kyakkyawan tabbacin zezo wata rana a watan gaba).
To kunga “Some Day” ta banbanta da “Someday” dan kuwa ita “Some Day”, tanuna lokacin (watan kenan) amma kumaa ba a faɗi ranar ƙararaba (afili) dan kugane cewa ba asan ranar ba kenan.
Misali (ii) ;
They scheduled the meeting some day, this week but I couldn’t remember when exactly it is.
(Sun saka ranar zaman a satin nan amma bazan iya tina takamammen wacce ranace ba) .
MENENE MA ANAR ONE DAY?
“ONE DAY” dai idan kun lura kalmomine guda biyu “One “ dakuma “day”
Duba kalmomin ɗaya bayan ɗaya.
“One” dai kalmar (Adjective) ce, sa annan kuma “Day” noun ce.
Awanann ɓangaren kalmar “One” tana nunine ga wani abu da za a yi a gaba amma ba a bayyana dai dai lokacin ba (ba ayanke sha warar yaushene neba) .
Kalmar “One” Ana iya amfani da ita dan nuni ga abun daya faru abaya kokuma wanda ze faru agaba (Past or future).
Misali ;
Idan mutum yace (“I did something One Day” ko “One Evening”) da dai sauransu to yana nufin yariga da yayi abunne.
Misalin (i)
“One Day” a matsayin (past);
One day, we had a terrible argument with him.
(Wata rana munyi musu me tsanani dashi)
(Watarana mun tafka muhawara dashi)
Toh kunga wannan ai (Past) ne ana nunine ga watarana amma wadda tariga da ta wuce (sa anan kuma ba a tabbatar da ranar ba) abayan.
Misali (ii) ;
One evening Ahmad phoned me.
(Wani yammaci Ahmad ya kirani)
To kunga anan an nuna abun yawuce tinda an rigada anyi kiran, (kuma ba a bayyana wane yammaci bane) .
Misalin (i)
“one day” amatsayin (future)
We should visite her one day.
(Yakamata mu ziyarce ta wata rana).
Wannan shikuma ai kunga aikin (lamarin) be faruba tukun ko.
MENENE BANBANCIN SOMEDAY DAKUMA ONE DAY?
Ku sani cewa tsakanin ma’anar “One Day” dakuma “Someday” duk kusan ɗaya ne duk da cewa “Someday ” ɗin ahaɗe take.
Sedai kuma “One day” tafi nuna kuduri me ƙarfi wato kamar wani alƙawari ne haka ko kuma abu wanda yake yiwuwarsa ba ze zama da sauƙi ba.
Misali (i)
One day, no human being will go hungry!
(Wata rana ba wanda ze zauna cikin yunwa)
(Wata rana ba wanda ze kasance me jin yunwa)
Misali (ii)
One day, the situation in my country would be settled.
(Wata rana komai ze dedeta a ƙasa ta)
Anan anfaɗi hakan ne da ƙudiri me ƙarfi na sa rai da hakan
“One Day” tafi nuna abin da ace lokacin faruwar sa sedai Allah yasani.
Faɗin hakan ze kasancene kamar abu ne wanda Allah ne ke da ikon yinshi kawai.
Ko kuma idan bai danganci (Nature) ba, to yana nuna alƙawari ne me girma (wato sa raine me ƙarfi)
Misali (i)
I will ensure your freedom one day.
(Zan tabbatar da ka samu enci wata rana)
You would certainly make it one day.
(Wata rana zaka cimma gaci)
(Wata rana zaka kai ga ci)
Amma ita ko “Someday” ba wai tana nuna ƙudiri kamar hakan bane
saboda yawanci ita tana nuna abu ne wanda baya buƙatar yunƙuri na musamman duba ga “One day”
Someday, Zarah will come.
(Wata rana, Zarah zata zo)
Idan Kun lura ai wannan be nuna wani abu na musamman ba.
Anan zan dakata
Idan akwai me tambaya yayi