Yanda ake anfani da Capital letter (Using Capital Letters)
Misali kamar “A” wannan itace capital letter , idan munaso mu rubuta karamin harafin “A” shine “a”.
Darasin namu zamuyi magana ne akan wuraren da akeyin amfani da capital letters.
Yawancin proper noun akan fara rubuta kalmar shine da babban harafi, Saboda proper noun sunaye ne na mutane, gurare (places), Kamfanuka (Companies), Littattafai (Books), Masana’antu, watanni (Months), Yawancin waɗannan sunayen da muka lissafa duka akan rubuta farkon haruffan su ne da Babban harafi (Capital letter). Misali
- Abdulmaleek
- Abdullahi
- Usman
- Mohidden
- Ahmad
- Auwal
- Khadijah
- Fatima
- Maryam
- Rukayya
Places
- Kaduna
- Zaria
- Bauchi
- Katsina
- Kano
- Adamawa
Companies
- Amazon
- Mercedes
Books
- In Search of Lost Time
- One Hundred Years of Solitude
- To Kill a Mockingbird
- Harry Potter and the Chamber of Secrets
Movies
- Captain America
- Love Actually
- Baywatch
Months/Days
- January
- February
- March
- Monday
- Tuesday
- Wednesday
Kamar dai yanda kaga mun jero sunayen dake sama wanda dukkan su Proper noun ne da ake fara rubuta su da Capital letter, Sai dai kuma idan kun lura zakuga idan muka haɗa gungun kalmomi guri guda zakuga akan samu wasu kalmomi a cikin su waɗanda ba’a fara rubuta su da Capital letter, Bari muyi misali da sunan wannan littafi na “The Lord of the Rings” zakuga yana da kalmomi guda biyu da ba’a fara rubuta farkon kalmar da Capital letter wato “of” da kuma “the” dalilin da yasaka ake rubuta su da small letters saboda sun zo ne a tsakiya, sannan kuma basu da wani muhimmanci a cikin Tittle din
Ga wasu daga cikin guraren da ake amfani da capital letters.
1. Anayin amfani da Capital letter a kowani farkon Jimla (sentence). Misali:
A wannan Jimlar “T” itace capital letter.
2. Anayin amfani da capital letter akowani farkon Sunayen mutane. Misali:
3. Anayin amfani da capital letter idan za’a rubuta sunan ubangiji (wato Allah).
4. Anayin amfani da capital letter a Haruffan abbreviation. Abbreviation yana nufin kamar takaita doguwar kalma ko Jimla ko sunan wani Abu, kamar sunan kungiya, Ma’aikata, makarantu, da dai sauran su. Misali:
A.B.U yana nufin (Ahmadu Bello University)
U.S.A yana nufin (United State of America)
5. Anayin amfani da capital letter a farkon harafin direct speech (direct speech shine maganar da aka kawota kamar yanda mai maganar ya fada ba canza koda harafi). Misali :
“She has not paid her school fees”, the teacher said – “Bata biya kudin makaranta ba “, malamin yace
6. Anayin amfani da capital letter a farkon Sunayen littafi Mai tsarki. Misali:
7. Anayin amfani da capital letter a kowani farkon Sunayen garuruwa. Misali:
8. Anayin amfani da capital letter a farkon Kalmar gaisuwar bude wasika. Misali :
9. Anayin amfani da capital letter a harafin kalmar gama wasika. Misali
10. Anayin amfani da capital letter a kowani farkon Sunayen ranaku da watanni. Misali:
11. Anayin amfani da capital letter a Tittle/heading na rubuta wasikar formal letter. Wato a Formal letter Kafin ka fara rubuta wasikar, sai ka fara fadin abinda yasa zaka rubuta wasikar. To akan rubutane da capital letter, wani lokaci kuma akan ja masa layi akasanshi. Misali :
12. Anayin amfani da capital letter a farkon harafin Kalmomin proper nouns (proper noun shine Sunayen kebabbun abubuwa na musamman na mutane da gurare, kamar garuruwa, kasashe wanda ko yaushe yake farawa da babban harafi). Misali:.