Menene Gerund Verbs a Hausa?
What is the meaning of gerund verbs in hausa?
Gerund verbs wasu kalmomin aikine wadanda akowani lokaci suke karewa da Haruffan “ing” galibi akanyi amfani dasu ne domin samar da suna (noun) daga cikin verb. Ga wasu daga cikin Kalmomin gerund verbs tare da ma’anoninsu
Wadannan Sune wasu daga cikin kalmomin gerund verbs, sai dai kuma zakaga kowanne kalma daga cikin Kalmomin gerund verbs suna karewa ne da “ing”.
Abin Lura anan shine zakaga da Present continuous tense da gerund verbs Kalmomin duk kusan iri daya ne (wato duk suna karewa da “ing) dalili kuwa shine, shi “present continuous tense” yana nuna mana aikin da ake yi yanzu ne shikuma gerund verbs yana nuna mana sunan abune kawai. yanzu alal Misali sai ince
Reading is the way of learning – Karatu shine hanyar koyo
kaga anan “reading” shine gerund verbs, abin mamaki zakaga Kalmar ta Kare da “ing” amma kuma ba “present continuous tense” bane. Idan kuma a present continuous tense zamuyi amfani da Kalmar “reading” ya koma “He is reading – yana karatu.
kaga a wannan Jimlar “reading” ya zama present continuous tense wato aikin da yakeyi yanzun ne yakeyi.
a gaskiya bambance tsakanin “gerund verbs” da “present continuous tense” yanada Matukar wahala ka fahimcesu lokaci guda, dole sai ka nutsu, kuma sai kayi tunani akansu sannan zaka fahimta, saboda zakaga Kalmomin iri daya ne haka zalika ma fassarar su duk dayane, Atakaicen takaitawa dai shi gerund verbs yana yanayimana nuni ne akan suna(noun), shikuma present continuous tense yana yi mana nuni ne akan aikinda akeyinshi yanzu, kadanna link din dake kasa domin karanta cikakken Darasin namu akan present continuous tense, ina fatan an fahimci Wannan Darasin, zamu dakata anan, idan anga gyara ko tambaya sai kayi mana comment a kasan Wannan posting din. Mun gode da ziyartar wannan shafin.
aslm alkm da fatan kuna nan lfy ina da tambaya game da gerund verb da kuma present partciple shi gerund verb in na fahimta ya na zuwa a farkon jimla shi kuma present participle yana zuwa a tsakiyar jimla