Banbancin sneak into da kuma sneak out to
Sneak into vs sneak out of
Sneak into ya na nufin wani mutum ya lallaɓa, ya shiga wani waje, ba tare da an ga shigarsa wajen ba.
Misali:
1. When I was very young, I would sneak into school if I was late.
Lokacin da na ke ƙarami, na kan lallaɓa na shiga makaranta idan na zo a makare.
2. Whenever I commit to my parents, I would sneak into house.
Duk lokacin da na yi wa iyayena laifi, na kan lallaɓa na shiga gida.
Sneak out of ya na nufin wani mutum ya lallaɓa, ya fita daga wani waje, ba tare da an ga fitarsa daga wajen ba.
Misali:
1. When I was very young, I would sneak out of our home at 7 o’clock.
Lokacin da na ke ƙarami, na kan lallaɓa na fita daga gidan mu ƙarfe 7.
Ka da dai a manta a yi subscribe ɗin channel ɗin mu mai suna Nura Mahadi da ke YouTube domin samun darusan koyan turanci cikin harshen Hausa.