What is the difference between come, coming, and came? (Hausa)
Sannan kuma zamuyi bayani akan yanda ake amfani da wadannan Kalmomin a cikin Jimla, Wanda da yawan Dalibai suna samun kura-kurai wajen amfani dasu
Come and coming
Ana iya amfani dasu ne a lokacin da ake aikata Aikin ko kuma anaso a aikata ko kuma an bada umarni a aikata
Come
Kalmar “Come” tana aiki biyu, zaka iya amfani da “come” ne lokacin da ake bada umarni ko kuma za’a aikata Aikin ba’a riga an aikata ba
i. Come here – zo nan/ kazo nan / kizo nan
Dukkaninsu umarni ne
ii. Come and give me spoon – Zo ka bani cokali.
iii. Come let go – Zo mu tafi
iv. Come and seat here – Zo ka zauna a nan.
Haka zalika zaka iya amfani da Kalmar “come” Idan zaka aikata Aikin da ba’a riga an aikata ba.
Misali:
i. I will Come to your house tomorrow – Zan zo gidanku gobe
ii. She will come next week – Zata zo sati mai zuwa.
Sannan kuma ana karawa “come” “ing” domin nuna cewa anayin aiki yanzu-yanzu
Coming
ana iya amfani da “coming” a lokacin da ake aikata Aikin (present continuous tense)
Misali :
I am coming to your house now – gani nan ina zuwa gidanku yanzu.
Came
Shikuma Kalmar “Came” anayin amfani dashine idan har an riga an gama aikata Aikin to za’ayi amfani da “came” ne.
Misali:
i. He came here this morning – yazo nan da safen nan
ii. I came to visit you – Nazone domin na ziyarceka.
iii. She came here to investigate – Tazo nan ne domin tayi bincike.
iv. I came early today – Nazo da wuri yau.
Wasu kura-kurai da Dalibai ke aikatawa har ‘yan Secondary school.
Idan umarni zaka bada Bazakayi amfani da “Came” ba, sai dai “Come”
Misali:
Idan kuma an riga an aikata Aikin, Bazakayi amfani da “come” ba, sai dai “Came”
Misali:
Bazakace “I come to greet you” (yin haka kuskure ne), sai dai kace “I came to great you – Nazo ne domin na gaida ka”
Haka zalika Bazakace “I come late today” ba sai dai kace “I came late today – Nazo a makare yau/Nazo latti yau” ko kuma kace “I came early today – Nazo da wuri yau”
Zan dakata anan, sai kuma a darasi na gaba idan Allah ya sake hadamu zamu cigaba, idan kanada tambaya ko neman Karin bayani sai kayi mana comment a kasan Wannan posting din