Menene ma’anar regular verb? (Aikatau mai bin tsari)
Kalmomin regular verbs
A wannan darasin zamu yi shine akan yanda ake samar da past tense ko past participle na regular verbs
Menene regular verbs?
Regular verbs sune jerin wasu kalmomin Verbs da ake samar da Past Tense dinsu ko kuma past participle nasu ta hanyar sanya haruffan “d, ied, ko kum ed” a karshen su
Hanyoyin da ake samar da regular verbs
1. Ana kara haruffan “ed” a karshen kalmar Aiki (verb) domin samar da past tense nasu. Bugu da kari, Idan kalmar aiki (verb) ta kare da harafin “e”, kawai zamu karawa kalmar “d” ne domin ta zama past tense. gamisali:
- Bake – yana nufin “gasa abinci”
- Baked – an riga an gasa abincin
- Work – yana nufin “Aiki”
- Worked – an riga anyi aikin
ALSO READ: Bambanci tsakanin It’s da kuma Its a cikin karatun turanci
2. Idan kalmar aiki (verb) ta kare da harafin “y”, to zamu canza harafin y din, sai mu sanya harafin “i”, sannan kuma sai mu sanya haruffan “ed” a karshen kalmar. misali:
- Dry – yana nufin “bushe”
- Dried – wanda ya riga ya bushe
- Apply – yana nufin “yin amfani da abu”
- Applied – abinda akayi amfani dashi
3. Idan kuma kalmar aiki (verb) wasali ne ya zo a bayan “y” din, kawai zamu kara haraffan “ed” ne, ba tare da mun cire harafin y din ba. Misali:
- Destroy – yana nufin “lalata”
- Destroyed – An lalata
- Play – yana nufin “wasa”
- Played – anyi wasa
Idan kuka lura da wadannan kalmomin dake sama zakuga wasali ne yazo kafin harafin “y” shiyasa ba’a canza y din ba gurin samar da past tense nasu
4. Idan kalmar aiki yazo da ga6a daya (one syllable), kawai zaka sanyawa kalmar irin harafin da take dauke dashi, su zama guda biyu, sannan sai ka sanya haruffan “ed” a karshe. Misali:
- Ban – yana nufin “hana”
- Banned – An hana
- Trap – yana nufin “tarko”
- Trapped – abinda aka samu sa’an shi
ALSO READ: Yadda ake amfani da kalmomin “were” da kuma “was” a cikin darasin turanci
5. Idan kuma kalmar aikatau yana da ga6o6i guda biyu (two syllables), to shima zamu sanyawa mishi irin harafin da yazo dashi na karshe su zama guda biyu (double consonants) tare da sanya haruffan “ed” a karshe. Misali:
- Permit – yarda ko amince
- Permitted – an yarda
- compel – Tilasta
- Compelled – an tilasta
Jerin Kalmomin regular verb tare da fassarar su a harshen hausa
Words | Regular verbs |
Accept – yarda | Accepted – an yarda |
Accuse – zargi | Accused – wanda ake Zargi |
Achieve – Samu | Achieved – An samu |
Act – aiki | Acted – anyi aikin |
Add – kara | Added – an kara |
Admire – martaba | Admired – an martaba |
Admit – amince | Admitted – an amince |
Adopt – amsar raining Yara |
Adopted – mutumin da aka Raine shi |
Affect – ta6a | Affected – an ta6a |
Advise – Shawara | Advised – anyi shawara |
Agree – amince ko Yarda |
Agreed – an amince |
Allow – bari | Allowed – an bari |
Announce – sanar | Announced – an sanar |
Appreciate – yabawa | Appreciated – an yaba |
Approve – amince | Approved – an amince |
Argue – yin gardama | Argued – Anyi gardama |
Arrive – iso | Arrived – an iso |
Ask – tambaya | Asked – an tambaya |
Assist – taimaka | Assisted – an taimaka |
Attack – farmaki | Attacked – an Kai farmaki |
Attempt – yinquri | Attempted – anyi yunquri |
Attend – halarta | Attended – an halarta |
Avoid – gujewa | Avoided – an guje |
Back – komawa baya | Backed – an koma Baya |
Bake – gasa abinci | Baked – an gasa abincin |
Banish – kora | Banished – an kora |
Decide – yanke shawara | Decided – an yanke shawara |
Deliver – isar | Delivered – an isar |
Demand – bukata | Demanded – an bukata |
Design – tsara | Designed – Wanda aka Tsara |
Destroy – lalata | Destroyed – lalatacce |
Develop – bunqasa | Developed – Wanda ya bunqasa |
Die – mutuwa | Died – matacce |
Disappoint – 6atawa wani Rai |
Disappointed – idan ran mutum Ya 6aci |
Discover – gano | Discovered – an gano |
Discuss – tattauna | Discussed – an tattauna |
Disregard – halin ko in kula | Disregarded – Wanda ba’a damu Dashi ba |
Disturb – takura | Disturbed – takurarre |
Divide – raba | Divided – Wanda aka raba |
Drag – ja | Dragged – Wanda aka ja |
Dress – sanya tufafi | Dressed – Wanda ya sanya Tufafi |
Dry – bushe | Dried – Busashshe |
Dunk – tsoma | Dunked – an tsoma |
Eliminate – kauda Abu A doron kasa |
Eliminated – wanda aka kashe |
Earn – samu riba | Earned – ribar da Aka samu |
Emigrate – yin hijira | Emigrated – anyi hijira |
Employ – daukar wani Aiki |
Employed – Wanda aka Dauka aiki |
Encourage – karfafa gwiwa | Encouraged – an karfafa gwiwa |
End – karke | Ended – na karke |
Enjoy – more | Enjoyed – an more |
Escape – ku6uta | Escaped – ku6utacce |
Beg – roqa | Begged – an roqa |
Behave – nuna halayya | Behaved – Mai hali |
Believe – imani | Believed – Mai imani |
Belittle – nuna cewa Abu bashi da muhimmanci |
Belittled – abinda aka nuna bashi da Muhimmanci |
Blame – daurawa wani Alhakin faruwar kuskure |
Blamed – Wanda aka dora masa Alhakin faruwar kuskure |
Boil – tafasa | Boiled – tafasashshe |
Borrow – aro | Borrowed – an ara |
Bother – damu | Wanda aka dameshi |
Bound – tsalle | Bounded – wanda yayi tsalle |
Brake – taka birki | Braked – an taka birki |
Bury – burne | Burried – an burne |
Call – kira | Called – an kira |
Carry – dauka | Carried – an dauka |
Cause – sanadi | Caused – Wanda yayi sanadi |
Celebrate – yin shagali | Celebrated – Wanda ake Matukar girmamawa |
Change – canji | Changed – an canja |
Chase – guje-guje | Chased – Anyi guje-guje |
Chat – hira | Chatted – anyi hira |
Cheat – cuta | Cheated – anyi cuta |
Check – bincika | Checked – an bincika |
Chew – tauna | Chewed – an tauna |
Clap – tafa | Clapped – an tafa |
Clean – tsafta | Cleaned – tsafta tacce |
Clear – sarai | Cleared – Wanda yake sarai |
Climb – hawa | Climbed – an hau |
Close – rufe | Closed – an rufe |
Coax – lallashi | Coaxed – anyi lallashi |
Collect – tattara | Collected – an tattara |
Compare – kwatanta | Compared – an kwatanta |
Compete – yin takura | Competed – an takura |
Complain – korafi | Complained – anyi korafi |
Concoct – girka abinci da Kayan abinci iri iri |
Concocted – abincin da aka girka Da kayan abinci iri iri |
Confess – amsa laifi | Confessed – an amsa laifi |
Construct – gina abubuwa | Constructed – abubuwan da Aka gina |
Contact – tuntu6a | Contacted – an tuntu6a |
Cook – dafa | Cooked – an dafa |
Copy – kwaikwaya | Copied – an kwaikwaya |
Cough – tari | Coughed – anyi tari |
Count – irga | Counted – an irga |
Crash – yin hatsari | Crashed – anyi hatsari |
Create – kirikira | Created – kirkirarre |
Cry – kuka | Cried – anyi kuka |
Curse – zagi | Cursed – an zagi |
Damage – ta’adi | Damaged – an lalata |
Dance – rawa | Danced – anyi rawa |
Estimate – kiyasta | Estimated – an kiyasta |
Expand – fadada | Expanded – an fadada |
Explain – yi bayani | Explained – anyi bayani |
Fish – kamo kifi | Fished – an Kama kifi |
Fix – gyara | Fixed – an gyara |
Flush – daure fuska | Flushed – an daure fuska |
Follow – bi | Followed – an bi |
Force – karfi | Forced – karfaffa |
Fry – soya | Fried – soyayye |
Gather – tattara | Gathered – tatta rarre |
Grab – damqe | Grabbed – an damqe |
Greet – gaisa | Greeted – an gaisa |
Guess – cinka | Guessed – an cinka |
Happen – faru/auku | Happened – wanda ya faru |
Harass – takura | Harassed – an takura |
Harm – illata | Harmed – an illata |
Hate – tsana | Hated – wanda aka tsana |
Heal – warkar | Healed – an warkar |
Help – taimako | Helped – an taimaka |
Hesitate – yin shakku | Hesitated – wanda akayi kokwanto |
Hope – tsammani | Hoped – abinda akayi tsammani |
Hunt – farauta | Hunted – abinda akayi farautar sa |
Hurry – yi sauri | Hurried – anyi sauri |
Identify – bayyanar da mutum |
Identified – an bayyanar da mutum |
Imagine – tunani | Imagined – anyi tunani |
Include – kunsa | Included – abubuwanda ya kunsa |
Insist – nacewa | Insisted – an nace |
Intend – kudurta | Intended – abinda aka kudurta |
Interest – sha’awa | Interested – abinda kake so |
Interrupt – katse hanzari | Interrupted – an katse hanzari |
Introduce – gabatar | Introduced – an gabatar |
Invent – kirkiro | Invented – an kirkiro |
Investigate – bincika | Investigated – an bincika |
Initate – fusata | Initated – an fusa ta |
Join – hade | Joined – an hade |
Jump – tsalle | Jumped – anyi tsalle |
Kick – buga abu da kafa |
Kicked – an buga abu da kafa |
Kill – kashewa | Killed – an kashe |
Knock – kwankwasawa | Knocked – an kwankwasa |
Kiss – sumbata | Kissed – anyi sumbata |
Laugh – dariya | Laughed – anyi dariya |
Learn – koyo | Learned – an koya |
Lie – karya | Lied – anyi karya |
Lift – daga | Lifted – an daga |
Link – hada | Linked – an hada |
List – jera abubuwa | Listed – an jera abubuwa |
Listen – sauraro | Listened – an saurara |
Live – rayu | Lived -an rayu |
Locate – sanya abu a wani guri |
Located – gurin da abu yake |
Lock – kulle | Locked – an kulle |
Love – kauna | Loved – abin so |
Measure – gwadawa | Measured – an gwada |
Murder – yin kisan kai |
Murdered – anyi kisan kai |
Mix – gauraya | Mixed – an gauraya |
Move – matsa | Moved – an matsa |
Note – rubutu | Noted – rubutacce |
Notice – lura | Noticed – an lura |
Obey – biyayya | Obeyed – anyi biyayya |
Offer – samar | Offered – an samar |
Open – bude | Opened – budadde |
Paint – fenti | Painted – anyi fenti |
park – pakin na abun hawa |
Parked – gurin da akayi pakin na abin hawa |
Pick – zabq | Picked – an zaba |
Phone – waya | Phoned – anyi waya |
Place – sanya abu a wani guri |
Placed – idan an sanya abu a wani guri |
Play – wasa | Played – anyi wasa |
Please – gamsar | Pleased – an gamsu |
Pluck – tsifa | Plucked – an tsefe |
Praise – yaba | Praised – an yaba |
Pray – addu’a | Prayed – anyi addu’a |
Prefer – son wani abu fiye da wani |
Prefered – abinda aka soshi fiye da wani |
Print – buga rubutu | Printed – rubutun da aka buga |
Promise – alkawari | Promised – alkawarin da akayi |
Pull – janyo | Pulled – an janyo |
Punch – naushi | Punched – idan akayi naushi |
Punish – hukuntar | Punished – an hukunta |
Purchase – siyayya | Purchased – siyayyan da akayi |
Question – tambaya | Questioned – an tambaya |
Race – yin gasa | Raced – anyi gasa |
Rain – ruwan sama | Rained – anyi ruwan sama |
Reduce – ragi | Reduced – anyi ragi |
Reply – mayar da martani |
Replied – an mayar da martani |
Request – Roko | Requested – an roka |
Retire – dena aiki saboda tsufa |
Retired – wanda ya dena aiki saboda tsufa |
Return – dawo | Returned – an dawo |
Scare – tsoratar | Scared – an tsorata |
Select – zabi | Selected – zababbe |
Share – raba abu ga wasu |
Shared – abinda aka raba ga wasu |
Shop – siyayya a shago |
Shopped – abinda aka siya a shago |
Sign – sa hannu | Signed – an sa hannu |
Slap – mari | Slapped – anyi mari |
Succeed – samun nasara | Succeeded – an samu nasara |
Suggest – hasashe | Suggested – abinda akayi hasashen sa |
Talk – magana | Talked – anyi magana |
Thank – gode | Thanked – an gode |
Touch – ta6a | Touched – an ta6a |
Try – kokarta | Tried – an kokarta |
Turn – juya | Turned – an juya |
Twist – murza | Twisted – an murza |
Type – rubuta | Typed – an rubuta |
Use – amfani | Used – mai amfani(past tense) |
Vary – Bambanta | Varied – wanda ya bambanta |
Vote – zabe | Voted – zababbe |
Wait – jira | Waited – an jira |
Walk – tafiya | Walked – anyi tafiya |
Want – bukata | Wanted – wanda aka bukata |
Warn – gargadi | Warned – wanda akayi gargadi |
Wash – wanke | Washed – wankakke |
Wish – bukata | Wished – wanda aka bukata |
Work – yin aiki | Worked – anyi aikin |
Worry – damu | Worried – an damu |
ALSO READ: SHAWARWARI GUDA 14 DA ZASU TAIMAKA WA MUTUM YA IYA TURANCI RANGADADAU
Wadannan wasu ne daga cikin kalmomin Regular verbs, amma kalmomin regular verb suna da yawa sosai,
Idan da akwai wani abu da baka gane ba a cikin wannan darasin kofa a bude take gurin yin mana tamba, domin yin maga tamaya saika duba comment section dake kasan wannan posting din, mukuma insha Allahu zamu yi kokarin baka amsarka alokacin daya dace