Mene ne present perfect continuous tense? | Shafin koyon turanci | Tenses|
Present perfect continuous tense in Hausa
Darasi akan present perfect continuous tense
Duk lokacin da muke so muyi bayani akan aikin da muke tayi tun abaya kuma har izuwa yanzu bamu gama ba, to zamuyi amfani ne da PRESENT PERFECT CONTINUOUS TENSE:
Daɗewar faruwar aikin zai’iya kasancewa:
Tun awa ɗaya da ya wuce izuwa yanzu.
- Tun sati biyu da suka wuce izuwa yanzu.
Tun wata 1, 2, 5, 8 da suka wuce har izuwa yanzu.
Ya danganta da irin aikin da kuma irin daɗewar da akan iyayi yi yayin gabatar da wannan aiki.
ALSO READ: Menene Ma’anar Nahawu (grammar) da turanci
THE PRESENT PERFECT CONTINUOUS TENSE: Ana amfani da shi ne yayin gabatar da aikin da ya daɗe yana faruwa a baya kuma sannan har izuwa yanzu.
Da farko zaka saka SUBJECT, sannan se ka saka HAVE BEEN/HAS BEEN, sannan sai ka saka VERB + ING (EAT + ING, = EATING)
SUBJECT + HAVE BEEN/HAS BEEN + VERB + ING.
Misali:
I HAVE BEEN WASHING. – NA DAƊE INA (TA) YIN WANKI./TINTINI NAKE (TA) YIN WANKI.
(HAVE)
I have been reading. = Na daɗe ina ta yin karatu/Tintini nake ta yin karatu. (Har izuwa yanzu)
We have been learning English. = Mun daɗe muna ta koyon Turanci/Tintini muke koyon Turanci. (Har izuwa yanzu)
They have been looking for you. = Sun daɗe suna ta neman ka/ki/ku/Tintini suke ta neman ka/ki/ku. (Har izuwa yanzu)
You have been sitting here. = Ka/kin/kun daɗe a zaune anan/Tintini ka/ki/ku ke zaune anan. (Har izuwa yanzu)
Haruna and Tijjani have been writing. = Ali da Ja’afar sun daɗe suna ta yin rubutu/Tintini Ali da Ja’afar suke ta yin rubutu.
(HAS)
She has been cooking today. = Tintini take ta yin girki yauɗinnan. (Har izuwa yanzu)
He has been working.
It has been running.
Ali has been typing.
ALSO READ: Me ake nufi da De Prefix a cikin karatun turanci?
THE PRESENT PERFECT CONTINUOUS TENSE POSITIVE QUESTION.
Duk lokacin da muke so muyi tambaya akan cewa: Shin ana tayin wani aiki tun abaya kuma har izuwa yanzu ba’a gama ba, to zamuyi amfani ne da PRESENT PERFECT CONTINUOUS TENSE POSITIVE QUESTION:
Daɗewar faruwar aikin zai iya kasancewa:
- Tun awa ɗaya da ya wuce kuma har izuwa yanzu.
- Tun sati biyu da suka wuce kuma har izuwa yanzu.
- Tun wata 1, 2, 5, 8 da suka wuce kuma har izuwa yanzu.
Ya danganta da irin aikin da kuma irin daɗewar da akan iya yi yayin gabatar da wannan aikin.
(HAVE) kokuma (HAS) zaka saka afarko sannan sai ka saka (SUBJECT) daganan sai ka saka (BEEN) se ka saka VERB+ING (eat + ing = eating.) Abu na ƙarshe shine: karka manta ka sanya alamar tambaya (?) a ƙarshen jimlar ka.
HAVE I + BEEN + GERUND VERB?
HAVE YOU + BEEN + GERUND VERB?
HAVE WE + BEEN + GERUND VERB?
HAVE THEY + BEEN + GERUND VERB?
ALSO READ: Menene Gerund Verbs a Hausa?
MISALI A CIKIN JIMLA
Have I been reading? = (Shin) Na daɗe ina ta yin karatu (kuwa)?/Tintini nake ta yin karatu (ne)? (Har izuwa yanzu)
Have we been learning English? = (Shin) Mun daɗe muna ta koyon Turanci (kuwa/ne)?/Tintini muke koyon Turanci (kuwa/ne)? (Har izuwa yanzu)
Have they been looking for you? = (Shin) Sun daɗe suna ta neman ka/ki/ku(kuwa/ne)?/tintini suke ta neman ka/ki/ku(kuwa/ne)? (Har izuwa yanzu)
Have you been sitting here? = (Shin) Ka/kin/kun daɗe a zaune anan(kuwa/ne)?/tintini ka/ki/ku ke zaune anan (kuwa/ne)? (Har izuwa yanzu)
Have Jamilu and Sunusi been writing? = (Shin) Jamilu da Sunusi sun daɗe suna ta yin rubutu(kuwa/ne)?/Tintini Jamilu da Sunusi suke ta yin rubutu(kuwa/ne)?
HAS HE + BEEN + GERUND?
HAS SHE + BEEN + GERUND?
HAS IT + BEEN + GERUND?
Has she been cooking today? = (Shin) Yau Tintini take ta yin girki (kuwa/ne)? (Har izuwa yanzu)
Has he been working?
Has it been running?
Has Ali been typing?