Me ake nufi da future perfect continuous tense a cikin karatun turanci?
Me ake nufi da future perfect continuous tense a cikin karatun turanci
LEARN TENSES: FUTURE PERFECT CONTINUOUS TENSE
Har yanzu muna cikin karatu ne akan Tenses, kuma muna bayani ne a karkashin “Future tense”, inda a darasin mu da ya gabata munyi bayani akan Future tense, da future continuous tense, da kuma future perfect tense, saboda haka a wannan darasin zamuyi bayani ne akan future perfect continuous tense
ALSO READ: Yadda ake amfani da Apostrophe a cikin jimla (Possessive S)
Menene antonyms a cikin karatun turanci? (Antonyms words)
Menene Future Perfect Continuous Tense?
Ana amfani da future perfect continuous tense ne don ya nuna aikin da ake hasashen zai faru nan gaba a siffar aikin daya wuce, zai ta faruwa, A takaice dai future perfect continuous tense aiki ne da zai faru, kuma ya cigaba da faruwa a lokaci mai zuwa
Ana samar da future perfect continuous tense ne ta hanyar sanya kalmar “will”, sai kuma a saka auxiliary verb na kalmar “have” sai a saka kalmar “been” daga karshe kuma sai a saka kalmar “present participle” (kamar dai yanda mukayi bayani a cikin wannan shafin, munce present participle sune kalmomin aiki da kowani lokaci suke karewa da -ing a karshen su)
ALSO READ: Menene Tenses a harshen turanci?
Yadda ake amfani da kalmomin “were” da kuma “was” a cikin darasin turanci
Yadda ake hada future perfect continuous tense a positive sentence
Da farko za’a saka “subject” a farkon jimla, sai a saka kalmar “will”, sai a saka kalmar “have”, sai asaka kalmar “been”, daga karshe kuma sai a saka kalmar “present participle”, ga formula a takaice: S + will + have + been + present participle, Bari mu kawo misali a cikin jimla
He will have been writing the book four month next week = Sati mai zuwazai riga ya dinga rubuta littafin tsawon wata hudu
He will have been studying English three years next month = wata mai zuwa zai riga ya dinga karatun English har tsawon shekaru uku
Yadda ake hada future perfect continuous tense a negative sentence
Da farko za’a saka “Subject”, sai a saka “will”, sai a saka “not”, sai a saka “been”, sai kuma a sakar kalmar present participle a karshe, Ga formula a takaice: S + will + not + have + been + present participle, bari mu kawo misali a cikin jimla
He won’t have been writing the book for four month next week = Sati mai zuwa ba zai riga ya dinga rubuta littafin tsawon wata hudu ba.
ALSO READ: HANYOYI (3) DA SUKE HANA MUTUM YA IYA TURANCI DA WURI
Yadda ake hada future perfect continuous tense a Qiestion form
Da farko zaka saka kalmar “will” a farkon jimla, sai ka saka “have”, sai kuma ka saka kalmar “been” daga karshe sai ka saka kalmar present participle, ga formula a takaice: Will + S + Have + Been + Present participle + …, bari mu kawo misali a cikin jimla
Will you have been writing the book for four month next week = Shin sati mai zuwa zai riga ya dinga rubuta littafin tsawon wata hudu?
wannan shine darasinmu na karshe akan tenses, idan kuka duba izuwa karatun mu na tenses zakuga wannan ne tense na goma sha biyu, kuma already munce muku tenses guda 12 muke dasu a cikin English, saboda haka wannan shine na karshe, sai dai abin da nakeso ku fahimta anan shine, Shi tenses sunayin kamanceceniya da junan su, kaga kuwa yafi kamata mai karatu ya maida hankali sosai da sosai wajen fahimtar bambance bambancen su, saboda haka ga fassarar kalmomin da suke cikin tenses a takaice:
- Simple = mai sauqi
- Present = Yanzu
- Continuous = mai cigaba
- Past = wanda ya wuce
- Perfect = cikakke
- Future = nan gaba
- Tense =lokaci
- Tenses = lokuta
Don neman karin bayani ko tambaya sai a same mu ta email din mu na Karatunturanci@gmail.com