Bambancin kalmomin dake karewa da -NCE da kuma -NT
Different Between Nt And Nce Words.
BAMBAMCIN KALMOMIN DAKE KAREWA DA -NCE DA KUMA -NT
Akwai kalmar dake karewa da -nce, wani lokaci kuma takare da -nt. Misali, dependence da dependent, ko importance da important, ko arrogance da arrogant, ko assistance da assistant.
Wadannan kalmomi kan rikita mutum har ya kasa bambamce da wacce ya kamata ya yi aiki a cikin rubutunsa.
ALSO READ: HANYOYI (3) DA SUKE HANA MUTUM YA IYA TURANCI DA WURI
Kalmomin dake karewa da -nce, kalmomine na suna. Sannan yawancinsu basu da plural, wato arrogance ba a cewa arrogances. Amma importance tanada plural wato importances.
Misali,
- Arrogance – girman kai
- Assistance – taimakawa/tayawa
- Importance – amfani/mahimmanci
- Patience – hakuri/jinya
- Difference – Bambanci
- Consequence – Saka mako
Su kuma wadanda ke karewa da -nt sifface ta suna.
Misali,
- Arrogant – mai girman kai
- Arrogants – masu girman kai
- Assistant – mataimaki/maitayawa
- Assistants – masu taimakawa/tayawa
- Important – mai amfani
- Importants – masu amfani/mahimmanci
- Patient – mai hakuri/majinyaci
ALSO READ: Me ake nufi da Regular Plural Noun a cikin karatun turanci
Misalai a cikin jumla
1. Aliyu is a self-reliance person.❌
Aliyu is a self-reliant person.✅
Aliyu mutumne mai dogaro da kansa
2. Fahad is a self-sufficient guy.
Fahad matashine mai wadatar zuci
3. Self-sufficience makes you zero-minded.
Wadatar zuci na sa ka rashin damuwa
4. We need his assistance.
Muna bukatar taimakonsa
5. He is my assistant.
Shine mataimakina
6. Eating fresh food is important to the health.
Cin lafiyaiyen abinci na da mahimmanci ga lafiya
7. Some of the importances of water, are: drinking, washing, cooking.
Wasu daga cikin amfanonin ruwa sune: sha, wanki da girki